27 Yuli 2019 - 06:52
Tawagar Ansarullah Ta Gana Da Jami’an Gwamnatin Rasha

Tawagar kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen bisa jagorancin Kakakin kungiyar Muhamad Abdul-salam ta isa birnin Moscow inda a jiya laraba ta gana da mataimakin ministan harakokin wajen kasar Mikhail Bogdanov da kuma wakilin shugaban kasar Rasha kan al'amuran da suka shafi gabas ta tsakiya.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran Pars ya bayar da rahoton cewa, a jiya laraba, tawagar kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta gana da manyan jami'an gwamnatin Rasha, inda suka tattauna kan rikicin kasar Yemen da kuma yarjejeniyar da aka cimmawa a kasar Sweden.

Tun a cikin watan Mayu na shekarar 2018 ne yarjejeniyar da aka cimmawa a kasar Sweden ta fara aiki dangane da batun tashar ruwan Alhudaida, domin zartar da wannan yarjejeniyar tun a ranar 11 zuwa 14 ga watan na Mayu Sojoji da dakarun sa kai na kasar Yemen suka kwashe dakarunsu daga lardin na Alhudaida, to sai dai Dakarun kawancen Saudiya a ko wata rana na karya yarjejeniyar.

Tashar ruwan Alhudaida ita ce babbar hanyar da ake shigar da taimako ga al'ummar kasar ta Yemen.




/129